Kakakin hukumar Sidiq Dersi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, mambobin hukumar 43 ne suka gana a wannan rana domin kada kuri'ar tsara kundin tsarin mulkin kasar, biyo bayan gyaran da mambobin hukumar suka yiwa wannan kundi.
Dersi ya ce bayan ganawar ce sai daruruwan masu bore suka yiwa hedkwatar hukumar zobe, don nuna rashin amincewarsu da wannan mataki. Sai dai an dauki dukkan matakan da suka dace don kare lafiyar mambobin hukumar da ke wannan ganawa.
Shugaban majalisar dokoki mai mazauni a gabashin kasar Libya Agila Saleh, ya yi kira ga zaman majalisar da ya auna irin rawar da hukumar dake rubuta kundin tsarin mulkin kasar take takawa. Yana mai jaddada bukatar a kafa kwamitin kwararru yayin da ake kokarin yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska, saboda gazawar hukumar na gabatar da daftarin kundin tsarin mulkin kasar. (Ibrahim Yaya)