Cikin wata sanarwar hadin gwiwa, bayan kammla ganawa kan yunkurin kawo karshen tashin hankali a Libya, Fayez Al Sarraj da Khalifa Haftar, sun ce sun amince su daina bude wuta tare da kauracewa amfani da dakaru kan duk wani abu sabanin yaki da ta'ddanci, bisa biyayya da yarjejenioyin siyasa na Libya da na kasashen waje.
Bayan matsalar siyasa da yakin basasa da suka shafe lokaci mai tsawo, shugabannin biyu sun lashi takobin kawo karshen rikicin Libya, wanda suka ce na bukatar wani tsarin sulhu na kasa da zai kunshi dukkan al'ummar kasar ciki har da cibiyoyin da rundunonin tsaro wadanda suka shirya a dama da su. (Fa'iza Mustapha)