in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin firaministan Sin ya kai ziyara Sudan
2017-08-26 16:40:56 cri
Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Gaoli, wanda a halin yanzu ke ziyarar aiki a kasar Sudan bisa gayyatar da aka yi masa, ya gana a jiya Jumma'a da shugaban kasar Omar Hasan Ahmad Al-Bashir da mataimakinsa kuma firaministan kasar Bakri Hassan Salih a birnin Khartoum, fadar mulkin kasar.

Yayin ganawarsa da shugaba Al-Bashir, Zhang Gaoli ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan Sudan wajen kiyaye mulkin kanta da cikakken yankin kasa, da kuma shimfida zaman lafiya a fadin kasar Sudan. Haka kuma, za ta ci gaba da yin mu'amala da kasar Sudan kan manyan harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

A nasa bangaren, Mr. Bashir ya ce, kasar Sudan za ta karfafawa kasashen Afirka gwiwar inganta hadin kan dake tsakaninsu da kasar Sin, bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka na FOCAC. Haka kuma, kasarsa za ta habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban-daban ciki har da na man fetur, ta yadda za a inganta dangantakar dake tsakanin kasashen bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon matsayi.(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China