in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar jiragen sama masu saukar ungulu ta kasar Sin dake aikin wanzar da zaman lafiya ta sauka a Darfur
2017-08-06 13:24:19 cri

Jiya Asabar jiragen sama masu saukar ungulu guda 2 suka sauka a filin jirgin sama na Al Fashir da ke yankin Darfur a yammacin kasar Sudan, wadanda suke cikin rundunar jiragen sama masu saukar ungulu ta farko ta kasar Sin.

Wadannan jiragen sama masu saukar ungulu 2 wadanda suke kula da aikin yin jigilar kayayyaki, sun dauki sojoji 15 da kayayyaki da injuna da nauyinsu ya kai ton 2. Sun tashi daga filin jirgin sama na Khartoum, sun dauki awoyi 4 suna kan hanya mai tsawon kilomita dari 9.

Bisa shirin da aka tsara, an ce, sauran sojojin kasar Sin da ke cikin rukunin share fagen, za su isa yankin Darfur cikin ragowar jiragen sama masu saukar ungulu 2 ba da dadewa ba. Sojojin kasar Sin da ke kula da ayyukan jigilar kaya da kafa sansani za su hadu, za su yi aikin sintiri a sama, da leken asiri a fagen yaki, da yin jigilar mutane, da kuma kaiwa wadanda suka jikkata a asibiti, kana da yin jigilar kaya da dai sauransu, bisa umurnin rundunar sojan musamman da MDD da kungiyar Tarayyar Afrika dake aiki a Darfur. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China