in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sin ta baiwa dailaban Ghana 65 guraben karo ilmi a makarantun kasar Sin
2017-08-17 10:23:55 cri
Da yammacin ranar Talata jakadar kasar Sin a kasar Ghana Sun Baohong, ta sanar da cewa, gwamnatin Sin ta bayar da guraben karo ilmi ga daliban kasar Ghana su 65 domin ci gaba da karatunsu a fannoni daban daban a wasu manyan makarantun kasar Sin a shekarar karatu ta 2017/2018.

Da take jawabi a wajen bikin liyafar ban kwana da aka shirya, wanda ta samu halartar dalibai 40 daga cikin daliban da suka amfana da tallafin karo karatun, Sun, ta bayyana farin cikinsa sakamakon karuwar yawan daliban kasar Ghana dake karatu a manyan makarantun kasar Sin.

Jakadar ta ce, kasar Sin ta dade tana karbar dalibai daga kasar Ghana tun a shekarar 1960. Kawo yanzu, jimillar dalibai 'yan kasar Ghana da suka samu tallafin karo ilmin daga gwamnatin kasar Sin sun kai 1,006. A halin yanzu, daliban kasar Ghana 5,516 ne suke karatu a kasar Sin, kuma wannan adadin ya nuna cewa Ghana ita ce ke sahun gaba tsakanin kasashen Afrika da suka fi yawan dalibai dake karatu a makarantun kasar Sin cikin shekaru uku a jere.

Ta ce gwamnatin kasar Sin tana ci gaba da samar da damammakin bada horo ga gwamnatin Ghana. A shekarar da ta gabata, 'yan kasar Ghana 1,200 ne suka amfana da shirin bada horo na gwamnatin Sin, kuma wannan adadi shi ne mafi yawa na 'yan kasashen waje da suka samu horo daga kasar Sin.

Jakada Sun, ta bukaci daliban da suka ci gajiyar shirin, da su kasance jakadu na gari bisa ga dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika a sabon karni. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China