Khan wadda ta bayyana hakan yayin da take yiwa taron manema labarai jawabi game da bunkasuwar tattalin arzikin duniya, ta ce alamu na nuna cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin za ta haifar da bukatar kayayyaki, zai kuma yi babban tasiri ga kayayyakin da ake samarwa a nahiyar Afirka.
Khan ta kuma ce tasirin ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin a kan tattalin arzikin Afirka kuwa, zai haifar da karuwar bukatar kayayyaki daga nahiyar Afirka. Ta kuma yi hasashen cewa, za a samu karuwar rukunin Sinawa masu matsakaicin kudaden shiga, sakamakon bunkasar tattalin arzikin kasar ta Sin, da karuwar kudaden shiga da kuma bukatar kayayyaki dake karuwa. (Ibrahim Yaya)