in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana: Za a fara amfani da na'ura mai kwakwalwa a tashoshin jiragen ruwan
2017-08-22 10:06:56 cri
Babban kwamishina a sashen tattara haraji na kasar Ghana Emmanuel Kofi Nti, ya ce kasar sa ta shirya fara amfani da dabarun tantance kayayyaki da ake shigarwa cikin kasar ta tashoshin jiragen ruwan ta, a wani mataki na ciyar da fannin gaba.

Mr. Nti wanda ke tsokaci game da wannan manufa, yayin wani taron horaswa da aka shirya game da fara aiwatar da ita, ya ce Ghana za ta fara aiki da wannan manufa ne tun daga ranar 1 ga watan Satumbar dake tafe.

Ya ce da zarar an fara bin wannan tsari, za a rika tantance kayayyaki, tare da tattara bayanai ta na'ura mai kwakwalwa, wanda hakan zai ba da damar kaucewa magudi daga bangaren jami'ai ko masu safarar hajoji.

Kaza lika Mr. Nti ya bayyana tsarin a matsayin hanyar rage jinkiri da ake samu wajen fiton kayayyaki, tare da kara yawan haraji da ake samu daga tashohin ruwan kasar. Har ila yau zai baiwa dukkanin hukumomin tsaro damar tantance kayayyakin da ake shigar da su cikin kasar cikin sauki, ba kuma tare da bata wani lokaci ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China