in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana na fatan hadin gwiwa da masu zuba jari a fannin sarrafa shara
2017-08-25 10:19:03 cri
Ministan ma'aikatar ruwa da tsaftar muhalli na kasar Ghana Kofi Adda, ya ce gwamnatin kasar sa na hadin gwiwa da masu zuba jari, domin zakulo hanyoyin sarrafa shara, da mayar da ita abubuwa masu amfani.

Burin dai a cewar ministan shi ne samar da makamashi, ko takin zamani, da robobin da ake iya sabuntawa daga bola. Ya ce hakan zai rage tarin bolar dake mamaye filayen da al'ummar kasar ke bukata.

Mr. Kofi Adda wanda ke zantawa da manema labarai a birnin Accra, ya ce hakan daya ne daga matakai da gwamnati ke dauka don cin gajiya daga harkar bola jari.

Tuni dai kasar Ghana ta samo tallafin kudi daga bankin Exim na kasar Sin, da wasu sauran sassa wadanda za a yi amfani da su wajen daga matsayin tsaftar muhalli a kasar. Bisa wannan tsari, kasar za ta yi amfani da bashin bankin Exim na kasar Sin har dalar Amurka biliyan 2, wajen gina dakunan sarrafa shara biyu biyu a daukacin yankunan kasar 10.

Ghana dai na fuskantar matsalar da shara ke haifarwa a kasar, inda a birnin Accra kadai ake tara tan 2,800 a ko wace rana. Kuma mahukuntan birnin na iya fidda kimanin tan 2,200 ne daga wannan adadi, yayin da ake barin kusan tan 600 wanda ke shiga magudanan ruwa, dake haddasa ambaliyar ruwa lokutan damuna.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China