Shugaban na Ghana, wanda ke ziyarar aiki ta kwanaki 3 a kasar Equatorial Guinea, ya yi kira da a karfafa hanyoyin cigaban kungiyar tarayyar Afrika (AU).
Yace, yayi amanna cewa saboda muhimmancin da rayuwar al'ummar nahiyar da yawansu ya kai biliyan daya da miliyan 200 ke dashi, dole ne shugabannin su tashi tsaye domin tabbatar da ganin an bunkasa tattalin arziki da siyasa, kuma a aiwatar da muhimman ayyukan da zasu tabbatar da dunkulewar nahiyar a zahiri.
Ya ce ana sa ran adadin al'ummar Afrika zai iya kaiwa biliyan 2 nan da shekaru 20 masu zuwa, akwai damammaki masu tarin yawa na harkokin cinikayya a fadin nahiyar.(Ahmad Fagam)