Sabon bankin kasashen Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afirka ta kudu wato BRICS, ya bayyana shirinsa na bude reshensa na yankin Afirka a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu cikin watan Maris mai kamawa.
Ministan kudi na kasar Afirka ta kudu Pravin Gordhan wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin da yake gabatar da kasafin kudin kasar a gaban majalisar dokoki, ya ce, Afirka ta kudu ta ba da kasonta na farko na dala miliyan 132 tun a watan Disamban shekarar da ta gabata.
Minista Gorghan ya ce, kasafin kudin kasar ya ba ta damar taka rawa a matsayin cibiyar harkokin kudi ta Afirka, matakin da zai baiwa hukumomi da masu sha'awar zuba jari daga nahiyar Afirka damar shiga a dama da su a harkokin kudi na duniya.
A watan Yulin shekarar da ta gabata ce rukunin kasashen na BRICS ya kaddamar da wannan bankin yayin taron kungiyar na 7 da ya gudana a birnin Ufa na kasar Rasha, a kokarin samar da kayayyakin more rayuwa, musamman a kasashe mambobin kungiyar ta BIRCS.(Ibrahim)