Kungiyar BRICS ta amince da shirin mai manufofi 7 ne yayin taron yini biyu na ministocin ciniki da masana'antu na kasashe mambobinta da ya gudana karshen makon da ya gabata a Hangzhou na kasar Sin.
Munufofin shirin na bunkasa hadin gwiwa a bangaren masana'antu tsakanin kasashe mambobin kungiyar su hada da: karfafa hadin kai ta fannonin ayyukan masana'antu tare da tsarawa da gama dabarun wuri guda da inganta sabbin kayayyakin aikin masana'antu da fadada hadin gwiwa a fannin bunkasa fasaha da kirkire-kirkire, da kuma kanana da matsakaitan sana'o'i.
Rob Davies ya ce shirin zai bada dama ta samu tare da musayar sabbin fasahohi ta hanyar samun jari daga kasashen waje, tare da gina karfin yin takara da sauran kasashen duniya. (F"aiza Mustapha)