in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta iya zama jigo wajen zamanintar da layukan dogo a Masar
2017-08-14 09:27:39 cri
Shugaban kungiyar sufuri ta Masar ETA Mohammed Shehata, ya ce kasar Sin za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen zamanintar da tsarin layin dogon kasar.

Ya ce kasar Sin ita ce ja gaba a wannan fanni, yana mai cewa, a shirye Sin take a ko da yaushe ta inganta kayayyakin more rayuwa a kasashe kawayenta.

Kungiyar ETA, babbar kungiya ce mai zaman kanta a Masar, wadda ke bibbiya tare da fitar da rahotanni game da tsarin sufuri a kasar dake arewacin Afrika.

Mohammed Shehata, ya ce kasar Sin na taimakawa kasashe da dama, musamman a Afrika wajen gina sabbi kuma nagartattun layukan dogo, yana mai jadadda cewa, babbar kasar ta nahiyar Asia ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen samarwa Masar kwararru a fannin shimfida layukan dogo da kuma harkar sufuri baki daya.

Har ila yau, ya ce gara kasar Sin ta gyara hanyoyin sufurin Masar a kan sauran kasashen nahiyar Turai, tun da baya ga kwararru da take da su, ta kan biya kudin aiki, sannan ta bada rangwamen farashi.

Ya ce ba kamar kasashen Turai ba, kasar Sin ba ita ke zabar kamfanonin da za su yi aikin ba. Sannan tana bada kudin ne ta hanyar rance daga bankunan kasar.

Mohammed Shehata ya kara da cewa, damawa da kasar Sin wajen sake gina layukan dogo a Masar, za ta taimaka wajen bunkasa shawarar "ziri daya da hanya daya" da zai hada Afrika da Asia. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China