Layin dogon na zamani wanda zai kai tsayin kilomita 66, na da tashoshi 11, zai kuma hade sabon yankin gudanarwa na birnin, ciki hadda biranen Al-Salam, da Ramadan 10, da Obour, da Badr da kuma Shorouk.
An sanya hannu kan wannan yarjejeniya ne tsakanin hukumar sufurin Masar NAT, da hadakar kamfanonin AVIC, da kamfanin China Railway Group Limited, a wani biki da ministan sufurin Masar Sherif Ismail, da jakadan Sin a kasar ta Masar Song Aiguo suka halarta.
Shugaban hukumar NAT Tarek Gamal El-Din, ya ce za a fara wannan aiki ne nan da watanni 2 zuwa 3 masu zuwa, kuma bayan kammalarsa, a kowace rana zai baiwa fasinjoji 340,000 damar sufuri ta jiragen kasan da za a samar, zai kuma rage tarin kudaden da Masar din ke kashewa a fannin sufuri.
Tun cikin watan Yuli ne dai shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya gana da wakilan kamfanonin na Sin, game da yadda wannan aiki zai gudana. (Saminu Hassan)