in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala babban zaben Angola
2017-08-24 11:06:21 cri

A jiya Laraba 23 ga watan nan ne aka gudanar da babban zaben kasar Angola, zaben da ya zamo karo na hudu tun bayan da ta samun 'yancin kai. Bayan zaben, shugaba mai ci Jose Eduardo Dos Santos, wanda ke kan karagar mulkin kasar tsawon shekaru 38 da suka gabata, zai sauka daga mukaminsa, to ko wane irin kalubale ne sabon shugaba mai jiran gado zai fuskanta? ko zai ci gaba da mai da hankali kan huldar dake tsakanin kasashen Sin da Angola a nan gaba?

A jiya Laraba ne aka bude rumfunan kada kuri'un babban zaben kasar Angola, inda masu kada kuri'un da suka yi rajista da yawansu ya kai miliyan 9 da dubu dari uku suka isa rumfunan da aka kafa a wurare daban daban a fadin kasar, domin kada kuri'unsu. Bisa dokar kasar ta Angola, shugaban kwamitin shirya zabe na kasar zai sanar da sakamakon karshe na babban zaben a cikin kwanaki 15 masu zuwa, tun bayan da aka kammala aikin kada kuri'un, haka ma shugaba mai ci Dos Santos, wanda ke kan karagar mulkin kasar tsawon shekaru 38 da suka gabata, zai sauka daga mukaminsa a hukumance a cikin wata guda, bayan da aka kammala aikin kada kuri'un.

Duk da cewa, 'dan takarar babban zaben na jam'iyya mai mulki a kasar wato jam'iyyar 'yantar da al'ummar kasar Angola, kuma tsohon ministan tsaron kasar Joao Laurenco shi ne zai lashe zaben, ya kuma maye gurbin shugaban kasar mai ci, ko shakka ba bu a yanzu lokaci bai yi ba tukuna na a tabbatar da hakan, amma ko shakka babu sabon shugaba mai jiran gado da aka zaba zai fuskanci wasu kalubaloli.

Mai nazarin harkokin kasashen Afirka dake aiki a cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa a Birtaniya Alex Vines yana ganin cewa, a halin da ake ciki yanzu, aiki mafi muhimmanci dake gaban sabon shugaban shi ne, kara kokari wajen raya tattalin arzikin kasar, tare kuma da rage dogaron kasar kan man fetur, yayin da take kokarin cimma burin bunkasa tattalin arzikinta. Ya ce, "Yanzu tattalin arzikin kasar Angola yana dogara ne kan man futer, wanda ya kai kaso 97 bisa dari, shi ya sa saurin ci gaban tattalin arzikin kasar ya gamu da matsala, saboda karyewar darajar farashin man fetur, kana adadin man fetur da kasar ta Angola ke samarwa zai ragu tun daga shekarar 2019, a saboda haka, wajibi ne sabon shugaban kasar ya samu wata sabuwar dabarar raya tattalin arzikin kasar a maimakon sayar da man fetur."

Ban da kalubale a fannin tattalin arziki, mai nazarin harkokin yammacin Asiya da Afirka dake aiki a cibiyar nazari kan zamantakewar al'umma, da kimiyya ta kasar Sin Zhou Jinyan tana ganin cewa, kamata ya yi sabon shugaban ya kara mai da hankali kan bukatun al'ummar kasarsa a fannin zaman rayuwa. Tana mai cewa, "A halin yanzu al'ummar kasar Angola kaso 60 bisa dari matasa ne da ba su kai shekaru 25 da haihuwa ba, kuma kafin babban zaben, jam'iyyar 'yantar da al'ummar kasar Angola ta taba yin alkawari cewa, za ta samar da guraben aikin yi dubu dari biyar gare su, to kuwa ya zama wajibi sabon shugaban da zai maye gurbin Dos Santos ya cika wannan alkawarin, kana abu mafi jawo hankalin jama'a shi ne batun yaki da cin hanci da rashawa. Idan sabon shugaban ya yi kokarin yaki da wannan matsala, tabbas zai tada hankalin masu hannu da shuni, wadanda ke da nasaba da iyalan shugaba Dos Santos. Ana iya cewa, wannan ne sabon kalubalen dake gabansa."

Kaza lika, Angola abokiyar cinikayya ce ta biyu ga kasar Sin a nahiyar Afirka. A halin da ake ciki yanzu, ko sabon shugaban kasar zai ci gaba da mai da hankali kan huldar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin? Zhou Jinyan na ganin cewa, lamarin ba zai kawo babban tasiri ga huldar dake tsakanin sassan biyu ba, amma yanzu haka wannan hulda ta gamu da matsala, kuma lokaci ya yi da za a kara kyautata ta domin samun sabon ci gaba. Ta ce, "A baya, an saba tsarin da aka amincewa, wato gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a ta hanyar sayar da man fetur, musamman ma a lokacin da kasar take shan matsalar yakin basasa, amma yanzu yanayin ya sauya, kasar ta Angola tana kara maida hankali kan ci gaban wasu sauran sana'o'i. Shi ya sa ya kamata a sake yin la'akari da huldar dake tsakanin Sin da Angola.

Mai nazarin harkokin kasashen Afirka dake aiki a cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa a Birtaniya Alex Vines shi ma ya amince da hakan, ya bayyana cewa, yanzu ana samun ci gaban tattalin arziki a Angola ta hanyoyi iri daban daban, huldar dake tsakaninta da kasashen waje ita ma tana bukatar yin sauye-sauye. Ya ce, "Huldar dake tsakanin Sin da Angola tana gudana yadda ya kamata, sassan biyu, suna gudanar da hadin gwiwa lami lafiya, ina ganin cewa, Angola ba za ta canja irin wannan hulda ba cikin gajeren lokaci, amma nan gaba kila Angola ta yi fatan kara kyautata huldar diplomasiyya dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, musamman ma bayan shekarar 2019, wato bayan da adadin man fetur da kasar ke samarwa ya ragu."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China