in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A yau ne za a gudanar da babban zaben kasar Angola
2017-08-23 10:40:02 cri

A Larabar nan 23 ga wata ne za a bude runfunan kada kuri'u a babban zaben kasar Angola, zaben da zai zamo irin sa na hudu da kasar za ta gudanar tun bayan da ta samu 'yancin kai, a kasar dake kudancin nahiyar Afirka. Abun da ya fi jawo hankalin jama'a shi ne za a zabi wani sabon shugaba a kasa ne da zai maye gurbin shugaba mai ci Jose Eduardo Dos Santos, wanda ke kan karagar mulkin kasar tsawon shekaru 38 da suka gabata.

Duk da cewa, bisa tsarin mulkin da aka zartas a kasar ta Angola a shekarar 2010, shugaba Dos Santos mai shekaru 75 da haihuwa, yana iya ci gaba da rike kan mukaminsa na shugaban kasar har wani sabon wa'adi na shekaru biyar, amma shi da kansa ya tsai da kudurin yin ritaya, kana ya bayyana cewa, ba zai zama shugaban jam'iyya mai mulki a kasar wato jam'iyyar 'yantar da al'ummar kasar Angola ba a shekarar 2018 mai zuwa.

To ko ina dalilin da ya sa ya yanke wannan kuduri? Ana tsammanin dai cewa, kila batun lafiyar sa ne, mai sa ido kan harkokin kasar Angola wanda ya yi shekaru da dama yana zaune a kasar Zhou Xiaoguo ya bayyana cewa, "Tun daga shekarar 2011, har zuwa bana, wato shekarar 2017, sau 7 shugaba Dos Santos na zama a kasar Spaniya bisa dalilai na kashin kansa, kuma ba ya sanar da lokacin tafiyar sa, ko na dawowarsa, kana a shekarar 2016, ya taba zuwa Spaniya sau biyu, bana ma haka abun yake, ya riga ya je Spaniya sau biyu; wato a watan Mayu da kuma watan Yuli, a watan Mayu kuwa, ya kasance a kasar ta Spaniya duk tsawon watan. A ranar 30 ga watan Mayun bana kuma, ministan harkokin wajen kasar ya fayyace cewa, ko shakka ba bu shugaba Dos Santos yana jinya a Spaniya, amma ya bayyana cewa, shugaban yana cikin koshin lafiya, zai kuma koma kasar ba tare da bata lokaci ba."

Ban da dalilin lafiyar jiki, mai nazarin harkokin yammacin Asiya da Afirka dake aiki a cibiyar nazari kan zamantakewar al'umma da kimiyya ta kasar Sin Zhou Jinyan tana ganin cewa, shugaba Dos Santos ya tsaida wannan kuduri ne domin kwantar da hankalin al'ummar kasar a halin da ake ciki yanzu, tana mai cewa, "Yanzu haka farashin man fetur ya ragu, a sanadin haka, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Angola bai wuce kaso 4 cikin dari kacal ba, a karkashin irin wannan yanayi, farashin kayayyaki a kasar ya karu bisa babban mataki, kuma al'ummun kasar da dama sun rasa aikin yi, hakan ya tada hankalinsu, saboda yawancin dukiyoyin kasar da ake samu ta hanyar sayar da man fetur suna hannun iyalan shugaban kasar, da wasu masu hannu da shuni, to amma idan shugaba Dos Santos ya sauka daga mukaminsa, kila hakan zai kwantar da hankalin al'ummar kasar."

A halin yanzu, jam'iyyar 'yantar da al'ummar kasar Angola za ta ci gaba da kasance babbar jam'iyya ta farko a kasar, dan takarar babban zaben na jam'iyyar, ana ganin kuma tsohon ministan tsaron kasar Joao Laurenco zai lashe zaben, ya maye gurbin shugaban kasar mai ci, to sai dai kuma ana da shakku kan rawar da zai taka bayan da ya dare kujerar shugaban kasar, duba da cewa diyar Dos Santos, wato Isabel Dos Santos ce shugabar kamfanin man fetur na kasar, wanda ke da babban tasiri ga tattalin arzikin kasar, kana dansa na farko kuwa shi ne shugaban asusun dukiyar kasar Angola, ban da haka kuma, shugaba Dos Santos shi ma ya yi sharar fage a fannin siyasa, Zhou Jinyan ta bayyana cewa, "Kwanan baya, majalisar dokokin kasar Angola ta zartas da wata sabuwar doka, inda aka tabbatar da cewa, ba za a gyara wasu kudurorin da shugaba Dos Santos ya kaddamar ba bayan da ya sauka daga mukaminsa, kana shugaban ya nada wasu jami'ai a wasu muhimman hukumomin kasar, duk wadannan matakai za su kayyade ikon mulkin sabon shugaban kasar."

Amma mai nazarin harkokin kasashen Afirka dake aiki a cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa a Birtaniya Alex Vines na ganin cewa, ko da yake a bayyana take shugaba Dos Santos zai ci gaba yin tasiri ga siyasar kasar ta Angola, amma babban zaben da za a yi a yau yana da babbar ma'ana, ya ce, "Duk da cewa, shugaba Dos Santos zai ci gaba da kasance shugaban jam'iyyar 'yantar da al'ummar kasar Angola na dan wani lokaci, amma tsarin ikon mulki a kasar zai sauya, shi ya sa ana iya cewa, babban zaben yana da ma'ana ga kasar, musamman ma ga al'ummar kasar ta Angola."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China