Kwanan baya, firaministan kasar Indiya Narendra Modi ya bayyana a yayin da yake ziyara a kasar Rasha cewa, ko da akwai sabani a tsakanin Sin da kasarsa kan batun iyakoki a tsakanin kasashen biyu, amma, cikin shekaru 40 da suka gabata, ba a taba yin musayar wuta a tsakanin kasashen biyu ba domin wannan batu.
Dangane da wannan lamari, malama Hua ta nuna cewa, kasar Sin tana maraba matuka kan bayanin da firaminista Narendra Modi ya nuna, a matsayin manyan kasashe guda biyu a duniya, ya kamata a kiyaye bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Indiya cikin himma da kwazo.
Bugu da kari, ta ce, a halin yanzu, kasashen Sin da Indiya sun dukufa wajen warware batun iyaka bisa tsarin ganawar wakilan musamman nasu, a sa'i daya kuma, an dauki matakai da dama domin kiyaye zaman lafiya da zaman karko a yankin iyaka. A nan gaba kuma, kasar Sin da kasar Indiya za su ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa fannoni daban daban domin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. (Maryam)