in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar hatsarin jirgin kasa a Masar ya karu zuwa 49
2017-08-12 12:53:49 cri
Gidan talabijin na kasar Masar ya ruwaito a jiya cewa, adadin wadanda suka rasu sanadiyyar hadarin jirgin kasa a lardin Alexandria ya karu zuwa 49.

A baya, Ma'aikatar lafiya ta kasar, ta sanar da cewa, mutane 36 ne suka mutu kuma sama da 120 sun jikkata sanadiyyar taho-mu-gama da wasu jiragen kasa biyu suka yi a gabashin birnin Alexandria.

Sai dai, Ma'aikatar ta ce adadin wadanda hatsarin ya rutsa da su ka iya karuwa la'akari da munanan raunuka da mutane suka samu.

Da safiyar jiya Juma'a ne, wani jirgin kasa da ya fito daga Cairo zuwa Alexandria, ya kutsa kai bayan wani jirgi da shima ke kan hanyarsa ta zuwa Alexandria, abun da ya yi sanadin mutuwa da jikkatar gomman mutane. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China