in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar za ta kafa yankin tattalin arziki na Golden Triangle
2017-08-03 11:20:59 cri
Majalisar zartaswar Masar ta amince da kudurin kafa yankin tattalin arziki na Golden Triangle a jiya Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na MENA ya ruwaito cewa, yankin na birnin Safaga dake gabar Bahar Maliya, zai kasance karkashen firaministan kasar Sherif Isma'il.

Wannan yunkuri, wani bangare ne na kokarin gwamnatin kasar na ci gaba da aiwatar da ayyukan raya kasa dake da nufin bada gudunmuwa wajen zuba jari a bangaren albarkatun yankin.

Kasar dake yankin arewacin Afrika, na yi wa tsarin tattalin arzikinta garambawul, al'amarin da ya samu kwarin gwiwa daga rancen dala biliyan 12 daga asusun bada lamuni na duniya IMF.

Masar ta kasance cikin matsin tattalin arziki cikin 'yan shekarun da suka gabata, sanadiyyar matsalolin siyasa da tsaro da suka haifar da raguwar zuwan masu yawon bude ido da masu zuba jari, a daidai lokacin da take tsaka da fuskantar gibin kasafin kudi da hauhawar farashin kayayyaki da kuma basussuka a ciki da wajen kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China