Mulatu Teshome ya bayyana haka ne a ranar Litinin, lokacin da yake ban kwana da Jakadan kasar Sin a Ethiopia mai barin gado La Yifan.
Da yake tsokaci game da muhimmiyar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu, shugaba Mulatu ya ce kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da kudin gudanar da manyan ayyukan ci gaba a Habasha.
Ya kara da cewa, hannun jarin kamfanonin kasar Sin a Habashan na ci gaba da karuwa inda yake samar da guraben ayyukan yi tare da kai wa kasar sabbin fasahohi.
Shugaban kasar ya ce shigar kamfanoni da masana na kasar Sin cikin ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa kamar layin dogon da ya tashi daga Habashan zuwa Djibouti, ya bada gagarumar gudunmawa ga ci gaban kasar.
A nasa bangare, Jakada La Yifan ya jinjinawa tagomashin da tattalin arzikin kasar ke samu cikin sauri, yana mai cewa, zai ci gaba da taimakawa wajen ganin dangantaka tsakanin kasashen biyu ta kara habaka. (Fa'iza Mustapha)