Wata sanarwar da ofishin Sarkin Morocco ya fitar, ta ce yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, Sarkin Morocco Muhammad na 6 da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, sun bayyana gamsuwa da ci gaban da ake samu ta fuskar musayar bayanai da ayyuka da suka shafi muhimmin aikin.
A watan Decemban bara ne kasashen biyu, suka kaddamar da gagarumin aikin da zai mika ya tunkari Turai, wanda kuma ke da nufin samar da hadin kai tsakanin arewaci da yammacin Afrika, da ba su damar samun makamashi mai zaman kanta, da gaggauta aiwatar da ayyukan samar da lantarki da kuma inganta tattalin arziki da ayyuakan masana'antu.
Ba a sanya wani lokaci na fara aikin shimfida bututun ba, haka zalika ba a bayyana nawa aikin zai lakume ba, sai dai, an gudanar da wasu taruka biyu kan aikin a Morocco. (Fa'iza Mustapha)