Zouiten ya bayyana cewa, yayin da sarkin kasar Morocco Mohammed na shida yake ziyara a kasar Sin a shekarar 2016, ya sanar da cewa, tun daga ranar 1 ga watan Yuni na shekarar, an soke visa ga masu shiga kasar daga Sin. Bayan kuma fara aiwatar da wannan manufa, yawan Sinawa dake zuwa kasar Morocco yawon shakatawa ya karu sosai.
Karuwar Sinawa dake zuwa kasar Morocco yawon shakatawa, na da babbar ma'ana ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar.
Bisa wata kididdiga ta hukumar yawon shakatawar kasar Morocco, yawan kudin da Sinawa ke kashewa a kasar Moroccon, ya kai ninka biyu bisa na al'ummun nahiyar Turai, kuma yawan kudin shiga da aka samu daga sha'anin yawon shakatawa ya kai kashi 9 zuwa 10 cikin dari, cikin jimillar dukkanin GDPn kasar. (Zainab)