Daraktar ofishin asusun dake yankin yammaci da tsakiyar nahiyar Afirka Marie Pierre Poirier, ta jaddada a cikin sanarwar cewa, tilas ne bangarori daban daban da rikicin ya shafa, su tabbatar da kiyaye hakkin kananan yara, da kare su daga cin zarafi, da tabbatar da tsaron makarantu da hukumomin kiwon lafiya, da amincewa ma'aikata masu aikin jin kai samar da gudummawa ga jama'a, ba tare da fuskantar wasu matsaloli ba. (Zainab)