in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da kisan jami'an sa a Congo Kinshasa
2017-03-30 13:58:48 cri
Kwamitin sulhun MDD ya fidda wata sanarwa a daren jiya Laraba, inda cikin ta ya yi Allah wadai da kisan wasu kwararrun jami'an MDD biyu a kasar Congo Kinshasa. Sanarwar ta kuma jaddada cewa, mai yiwuwa a dauki wannan ta'asa a matsayin laifin yaki.

Kwamitin sulhun ya kuma kalubalanci gwamnatin kasar Congo Kinshasa, da ta gaggauta bincike kan wannan lamari, tare da damke wadanda suka aikata shi.

Da yake bayyana matsayar sa game da lamarin, babban magatakardar MDD António Guterres, ya bayyana cewa, MDD na bincike game da wannan lamari don tabbatar da adalci.

A ranar 28 ga watan nan ne MDD ta bayyana cewa, ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD sun gano gawawwaki biyu, na mambobin rukuni na masanan na MDD dake aiki a kasar Congo Kinshasa.

An gano gawawwakin ne a ranar 27 ga wata a birnin Kananga dake kudancin kasar Congo Kinshasa, daga baya an bayyana sunayen mamatan wato Michael Sharp dan kasar Amurka, da Zaida Catalan dan kasar Switzerland, wandan da aka yi garkuwa da su a daren ranar 12 ga wannan wata a jihar Kasai-Central.

An ce an yi garkuwa da turawan ne tare da wasu 'yan kasar Congo Kinshasa 4 dake tare da su, amma ya zuwa yanzu ba a san inda sauran mutanen suke ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China