Zuwa yanzu an gano mutane 19 wadanda ake shakkar ko sun kamu da cutar ta Ebola a kasar Congo Kinshasa, cikinsu kuma tuni 3 suka mutu. Ganin haka ya sa kungiyar samar da allurar rigakafin cututtuka ta kasa da kasa, ta tanaji allurar rigakafi guda dubu 300 wadda kamfanin Merck ya samar, sai dai kafin a fara amfani da su, ana bukatar samun izini daga hukumar ta WHO.(Bello Wang)