Wani jami'i a birnin ya tabbatar da cewa, a jiya da yamma, fursunonin kurkukun tsakiya na birnin Bukavu, sun tada da bom inda suka yi amfani da shi wajen tserewa daga kurkukun, ya na mai cewa, daga bisani 'yan sanda sun yi kokarin kama su.
Jami'in ya kara da cewa, fursunoni fiye da 20 sun tsere, yayin da wasu 3 suka mutu a lokacin da 'yan sanda ke kokarin kama su, kana wasu sun ji rauni.(Zainab)