in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yaba da aikin da rundunar tabbatar da zaman lafiya ta kasar Sin dake kasar Sudan ta kudu ta yi
2017-08-19 12:48:33 cri
Rundunar tabbatar da zaman lafiya ta kasar Sin dake kula da ayyukan injiniya a kasar Sudan ta kudu, ta kammala aiwatar da sabbin ayyukan more rayuwa ga kungiyar musamman ta MDD dake zaune a yankin da ake yaki a yammacin Sudan ta kudu.

Sakamakon haka ne rukunin tantance ingancin aikin na kungiyar musamman ta MDD dake kasar Sudan ta kudu ya yaba wa rundunar, yana mai bayyana aikin a matsayin wanda ya warware matsalolin rashin wurin kwana da na rayuwa da sojoji da kuma ma'aikatan MDD suke fuskanta.

A 'yan watannin nan, halin da ake ciki a kasar Sudan ta kudu ya kara tsananta, har ma a kan samu rikice-rikice a tsakanin bangarori masu adawa da juna, al'amarin ya sa yawan 'yan gudun hjira ke ta karuwa. Ana bukatar sabuntawa ko kuma gyara tsoffin dakunan kwana da na ba da kariya dake cikin sansanin MDD domin tinkarar halin tsaron da yake tsananta.

Sabo da haka ne, sojojin injiniya na kasar Sin, suka hanzarta aikin gina dakunan kwanan, abun da ya dauke su watanni shida kacal wajen kammala aikin samar da sabbin dakunan kwana 54, don tabbatar da ganin MDD ta gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China