in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci a baiwa kananan yara kariya a Sudan ta kudu
2017-07-09 11:56:26 cri
Asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF, ya bukaci a samar da kariya ga yara kanana a daidai lokacin da Sudan ta kudu ke shirin bikin murnar cika shekaru 6 da samun 'yancin kai a yau Lahadi.

A cikin wata sanarwar da wakilin UNICEF dake Sudan ta kudu Mahimbo Mdoe ya fitar a Juba, ya ce a yayin da kasar ke murnar cika shekaru 6 da samun 'yancin kai a ranar 9 ga watan Yuli, fata da kuma burin da ake da shi game da kananan yara ba'a cimma shi ba a kasar, inda sanarwar ta bayyana irin halin da yara kanana ke ciki a Sudan ta kudun da cewa rayuwa ce ta tashin hankali.

Hukumar tallafawa kananan yaran ta bayyana cewa, yara a kasar na ci gaba da fuskantar tashin hankali da tabarbarewar muhimman al'amurran da suka shafi rayuwarsu, tana mai nuni da cewa kusan dukkan abubuwan da suka shafi hakkokin yara kananan ba'a bayar da su a Sudan ta kudun ba.

UNICEF ta kara da cewa, a yayin da take ci gaba da kara kokarin samar da tallafin gaggawa ga wadanda ke cikin matsananciyar bukatar daukin gaggawar, har ila yau hukumar tana ta kokarin ganin kananan yara sun samu tsaro da kwanciyar hankali a kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China