in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan tawayen Sudan ta kudu sun sake kwace iko da Pagak daga hannun sojojin gwamnati
2017-08-14 13:39:49 cri
'Yan tawayen Sudan ta kudu sun sanar da sake kwace iko da hedkwatar Pagak daga hannun dakarun gwamnatin kasar, wanda a baya yake hannun sojojin kasar Sudan ta kudu.

Mai magana da yawun 'yan tawayen kwatar 'yancin Sudan, dake nuna biyayya ga tsohon mataimaki na farko ga shugaban kasar Sudan ta kudu Riek Machar, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai an Xinhua daga maboyarsu cewa, yanzu su ne suke da iko da garin Pagak dake kusa da kan iyakar kasar Habasha.

Kasar Sudan ta kudu dai ta fada cikin tashin hankali ne a watan Disambar shekarar 2013, bayan barkewar rikicin siyasa tsakanin shugaba Kiir da tsohon mataimakinsa Machar, lamarain da ya haifar da fada tsakanin sojojin dake biyayya ga jagororin biyu.

Sai dai kuma a watan Yulin shekarar 2016, sassan biyu sun keta yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekarar 2015, da nufin kawo karshen tashin hankalin da ya barke a kasar, lokacin da wani sabon fada ya barke a Juba, babban birnin kasar tsakanin dake gaba da juna, abin da ya tilastawa Machar yin gudun hijira.

Fadan da ya barke a kasar ya haddasa mutuwar dubban mutane, baya ga wasu miliyoyi da rikicin ya tilastawa yin gudun hijira. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China