Yayin wani taron manema labarai a jiya Laraba, wakilin UNICEF a Sudan Abdullahi Fadil, ya ce karuwar kwarar 'yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu da sama da mutane miliyan 2.3 da suka gujewa muhallansu a cikin kasar, na karawa al'ummomin da ke karbarsu nauyi.
Ya kara da cewa, yara ne ke ci gaba da fadawa haddura, kuma samun taimako mai dorewa na da mutukar muhimmanci wajen kai musu dauki a kan lokaci da samar da kayayyakin jin kai musamman ruwa da kayayyakin tsaftace muhalli da na kiwon lafiya da kuma sinadaran gina jiki. (Fa'iza Mustapha)