in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matasa a Sudan ta kudu na hankoron wanzar da zaman lafiya
2017-08-07 09:36:25 cri
Wasu gungun matasa a kasar Sudan ta kudu, sun rungumi matakan raya al'adu a matsayin hanyar dakushe nunawa juna wariya, tare da wanzar da zaman lafiya a kasar da tashe tashen hankula suka daidaita.

Matasan dai na shirya bukukuwa na kade kade da raye raye, da nuna fasahohin zane zane, da wasannin kwaikwayo, da na ban dariya, domin kau da tunanin 'yan kasar daga rarrabuwar kawuna da kin jinin juna.

Wata matashiya mai sana'ar waka mai suna Varna Joseph ta bayyana cewa, ta shiga wannan tsari ne, ganin irin halin damuwa da iyaye ke shiga sakamakon hallaka 'ya'yansu da ake yi yau da kullum, da ma yadda yunwa ke yiwa al'ummar kasar kisan mummuke. Ta ce manufar su ta jawo hankulan kowa da kowa zuwa ga kaucewa rura wutar rikici.

Varna Joseph ta kara da cewa, tana amfani da wakokinta wajen ilmantarwa, da fadakar da jama'a game da hakkokinsu, da ma halin da matan kasar ke ciki na damuwa.

Mawakiyar ta ce muddin za a ci gaba da bayyana banbance banbance, da nuna yatsa ga juna tsakanin kabilun kasar, ko shakka babu ba za a cimma nasarar da ake bukata ta wanzar da zaman lafiya da hadin kai ba. Don haka a cewarta ya zama wajibi, dukkanin sassa su yi aiki tukuru wajen tabbatar da kafuwar irin kasar da suke fata, mai cike da zaman lafiya da lumana. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China