in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kudu ta zargi 'yan tawaye da haddasa matsalar tsaro a kan iyakokin kasar
2017-07-05 10:24:12 cri
Kakakin sojojin kasar Sudan ta Kudu Santo Domic Chol ya zargi 'yan tawaye da haddasa matsalar tsaro a kan iyakar kasar da kasar Uganda, wadda a halin yanzu sama da 'yan gudun hijirar Sudan ta kudu miliyan 1 ke zaune a ciki.

Santo ya bayyana hakan ne sakamakon wasu rahotanni da ke cewa, wasu 'yan tawayen Sudan ta kudu na shigar bulta suna sace 'yan gudun hijira tare da kwashe masu dabbobi a sansanonin 'yan hijira dake gundumar Moyo na kasar Uganda.

A watan Disamban shekarar 2013 ne dai kasar Sudan ta kudu ta fada cikin tashin hankali, bayan wata takaddamar siyasa da ka kaure tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar, lamarin da ya haifar da mummunan fada tsakanin sojojin dake biyayya ga shugabannin biyu.

Sai dai yarjejeniyar zaman lafiyar da sassan biyu suka cimma a shekakar 2015, ba ta je ko'ina ba. Alkaluma na nuna cewa, fadan ya lakume rayukan dubban jama'a baya ga miliyoyin mutane da suka gujewa muhallansu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China