in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da Paul Kagame a wa'adin shuganbacin Rwanda na 3
2017-08-19 12:37:22 cri
An rantsar da Paul Kagame a matsayin shugaban kasar Rwanda a wa'adi na 3, jiya Jumma'a a Kigali, babban birnin kasar.

Paul Kagame ya karbi rantsuwar ne daga babban jojin kasar Sam Rugege, yayin bikin kaddamar da shi da ya samu halartar shugabannin da jami'an kasashen Afrika da suka hada da Kenya da Uganda da Ethiopia da Senegal da Gabon da Sudan ta kudu da Zambia da Niger da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Namibia da kuma Sudan.

A jawabinsa, Shugaba Kagame ya bayyana bikin karbar rantsuwar a matsayin ranar sabunta al'amura da nuna godiya.

Ya ce yana son yabawa shugabanni da mambobin jam'iyyun siyasa 8 da suka hade da Jam'iyyar RPF domin zabarsa a matsayin dan takararsu, yana mai cewa, sun hada hannu cikin shekaru 23 bisa mutunta juna domin gyara zamantakewar kasarsu da ke cikin mawuyacin hali.

Shugaba Kagame Ya ce su a Rwanda, za su ci gaba da ammana da hada gwiwa da kawaye daga fadin duniya.

Kimanin al'ummar Rwanda miliyan 6.9 ne suka kada kuri'a a zaben shugaban kasar da ya gudanar ranar 4 ga watan nan na Augusta, inda Paul Kagame ya lashe zaben da kashi 98.79 na kuri'un da aka kada yayin da dan takarar indipenda Philippe Mpayimana da ya zo na biyu da mai bi masa Frank Habineza na Jam'iyyar Democratic Green Party of Rwanda suka samu kasa da kashi 1 kowannensu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China