in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu sanya ido na shiyya sun yaba da yadda zaben shugaban kasar Rwanda ya gudana
2017-08-07 10:05:47 cri
Shugabannin tawagar masu sanya ido na Afrika (EOM) a zaben shugaban kasar Rwanda sun yaba da yadda zaben shugaban kasar na ranar Jumma'a ya gudana, inda suka bayyana shi da cewa an bi ka'idoji irin na demokaradiyya a zaben.

Shugabannin sa idon wadanda suka fito daga kungiyar kasashen gabashin Afrika (EAC), da kungiyar kasuwanci ta gabashi da kudancin Afrika (COMESA), da kungiyar hadaka ta kasa da kasa na manyan tafkuna (ICGLR), sun gabatar da rahotannin farko game da yadda suka ganewa idonsu yadda zaben ya gudana, yadda aka kada kuri'un da yadda aka tattara su.

COMESA ta yaba da irin kwarewar da jami'an hukumar zaben kasar suka nuna wadanda suka jagoranci gudanar da zaben wanda aka kammala cikin nasara.

Amma Bishop Mary Nkosi, wanda shi ne ya jagoranci tagawar masu sanya ido a zaben karkashin COMESA, ya bukaci a kara kudaden da ake warewa ga hukumar zaben kasar musamman wajen kara adadin shirin wayar da kan jama'a.

Sakamakon da hukumar zaben kasar Rwandan ta fitar a ranar Asabar ya nuna cewa, shugaban kasar mai ci Paul Kagame, ya samu kashi 98.63 na adadin kuri'un da aka kada a zaben, lamarin da ya ba shi nasarar sake zama shugaban kasar a karo na uku.

Kagame, mai shekaru 59, ya samu yawan kuri'u miliyan 6.6 a zaben.

Dan takarar shugaban kasar na indifenda Philippe Mpayimana, ya samu 0.73 cikin 100, sai kuma Frank Habineza, dan takarar jam'iyyar Democratic Green Party of Rwanda, wanda ya samu 0.47 cikin 100. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China