in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara zaben shugaban kasa a Rwanda
2017-08-04 20:29:27 cri

A Jumma'ar nan ne aka fara kada kuri'u, a zaben shugaban kasar Rwanda wanda masu fashin baki ke ganin shugaban kasar mai ci Paul Kagame ne zai lashi shi. Yanzu haka dai shugaba Kagame na takara ne domin sake dare kujerar shugabancin kasar a karo na 3 mai wa'adin mulki na shekaru 7.

Sama da rumfunan kada kuri'u 2,300 dauke da kusan mutane 17,000 ne ake sa ran za su fita kada kuri'u tun daga karfe 7 na safe, a kuma rufe rumfunan zaben da karfe 3 na yamma.

Baya ga shugaba Kagame na jam'iyyar RPF mai mulki, sauran 'yan takara a zaben sun hada da Frank Habineza na DGP, da kuma Philippe Mpayimana, wanda ke zaman dan takara mai zaman kansa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China