Sakamakon da hukumar ta fitar ya nuna cewa, Paul Kagame ya lashe zaben da kaso 98.66 na kashi na kuri'un da aka kada.
Abokan adawarsa da suka hada da dan takara mai zaman kansa Phillippe Mpayimana da Frank Habineza na jam'iyyar Democratic Green sun samu kaso kasa da 1, inda hukumar zaben ta ce masu kada kuri'a miliyan 5.5 daga cikin miliyan 6.9 ne suka yi zaben.
Paul Kagame wanda ya nemi mulki a karo na uku, ya mika godiya ga magoya bayansa, a lokacin da yake jawabi a hedkwatar jam'iyyarsa ta RPF.
Ya ce a bayyane yake cewa jam'iyyar RPF ce ke da nasara, yana mai jinjinawa magoya bayansa da suka sake zabarsa dan sake mulkin kasar a karo na 3. (Fa'iza Mustapha)