in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara yakin neman zaben shugaban kasa a Rwanda
2017-07-17 09:18:05 cri

A ranar Jumma'a ne aka fara yakin neman zaben shugaban kasa a kasar Rwanda, zaben da 'yan takara uku ciki har da shugaban kasar mai ci Paul Kagame ke neman lashe kujerar shugaban kasar.

Sauran 'yan takarar sun hada da Frank Habineza na jam'iyyar DGPR sai kuma Philipe Mpayimana a matsayin dan takara mai zaman kansa.

Hukumar zaben kasar (NEC) ta bayyana cewa, za a kammala yakin neman zabe ne a ranar 3 ga watan Agusta, kwana guda kafin ranar zabe.

Shugaba Kagame dai ya samu gagarumar nasara a zaben shekarar 2003 inda ya samu kaso 95 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da ya samu kaso 93 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben shugabancin kasar na shekarar 2010.

Sai dai 'yan adawa na kokarin janyo hankalin masu kada kuri'a yayin da Kagame ke kara samun goyon bayan 'yan kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China