Manajan bankin dake kasar ta Rwanda Yasser El-Gammal wanda ya bayyana hakan a birnin Kigali, fadar mulkin kasar, yayin bikin sanya hannu kan yarjejeniyar ba da rancen, ya ce ana fatan rancen zai taimaka wajen aiwatar da shirye-shirye da kasar ta tsara game da hakan,karkashin matakan kasar na raya tattalin arziki da kawar da talauci kashi na biyu(EDPRS2).
Bugu da kari, ana fatan rancen zai taimakawa kasar ta Rwanda cimma nasarar burin da ta sanya a gaba na samar da guraben ayyukan sama da 200,000 a bangaren aikin gona kamar yadda yake kunshe cikin kashi na biyu na shirin raya tattalin arziki da kawar da talauci na kasar.(Ibrahim)