Kwamitin sulhu na MDD ya jaddada cewa, ya kamata kasashen duniya su dukufa wajen hana yaduwar ta'addanci, domin kiyaye zaman lafiya da tsaron gamayyar kasa da kasa. Haka kuma, a gurfanar da wadanda suka aikata wannan laifi gaban kuliya.
Babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya fidda wata sanarwa ta bakin kakakinsa, wadda ke Allah wadai da harin na birnin Barcelona, yana mai cewa MDD tana goyon bayan gwamnatin kasar Spaniya wajen yaki da ta'addanci.
Haka kuma, hukumomin kungiyar tarayyar kasashen Turai, da wasu shugabannin kasashen na Turai sun fidda sanarwa a ranar 17 ga wata, inda suka soki harin na birnin Barcelona, a sa'i daya kuma, sun bayyana aniyarsu ta yaki da ta'addanci cikin hadin gwiwa. (Maryam)