in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Ghana ta tsara manyan manufofi da nufin farfado da bangaren masana'antun kasar
2017-08-15 09:58:56 cri
A jiya ne shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo na kasar Ghana ya zayyana wasu manyan tsare-tsare guda goma domin farfado da bangaren masana'antun kasar.

Wadannan manufofi sun hada da kara karfin masana'antun kasar ta hanyar samar musu da kafar samun rance mai matsakaici da dogon zango da babu kudin ruwa sosai, bullo da dabarun da za su taimakawa masan'antun ta yadda za su bullo da sabbin hanyoyin raya tattalin arzikin kasar ta Ghana, kafa a kalla rukunin masana'antu guda daya da yankin tattalin arzikin na musamman a dukkan shiyyoyin kasar guda 10.

Da yake jawabin yayin taron kolin tsara manufofin kasar karo na biyu a birnin Accra, fadar mulkin kasar, shugaba Akufo-Addo ya bayyana cewa, wadannan manufofi da shirye-shirye da ake fatan bullowa, za su samu tallafin wasu manufofi a matakin gwamnati ta yadda za su saukaka ci gaban sassan masu zaman kansu, baya ga samar da guraben ayyukan yi ga matasan kasar.

Ya ce gwamnati ta bullo da wasu shirye-shiryen raya masana'antu, musamman a bangaren sarrafa amfanin gona da samar da kayayyaki, da nufin raya tattalin arziki da samar da guraben ayyukan yi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China