in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Libya ya yi kiran da a gudanar da sabbin zabuka a kasar
2017-07-17 10:02:02 cri

Firaministan kasar Libya da MDD ke marawa baya Fayez Serraj ya yi kiran da a gudanar da sabbin zabukan majalisar dokoki da na shugaban kasa a watan Maris din shekarar 2018. Zaben da firaministan ya ce zai baiwa 'yan kasar damar zabar sabon shugaban kasa da 'yan majalisun dokoki, kuma zaben ba zai shafi yarjejeniyar siyasar kasar da MDD ke marawa baya ba.

An dai nada gwamnatin hadin kan kasar Libya da Serraj ke jagoranta ne bisa yarjejeniyar shimfida zaman lafiya da MDD ta gabatar da nufin kawo karshen rarrabuwar kawunan siyasar kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China