in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A Najeriya ASUU ta shiga yajin aiki don neman a ba ta wasu kudade
2017-08-16 11:12:11 cri
Kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya ASUU, ta fara wani yajin aiki na sai abin da hali ya yi domin neman gwamnati ta samar mata da karin kudade.

Daga cikin dalilan yajin aikin akwai bukatar da kungiyar ta nema na aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya tun a shekarar 2009.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa Biodun Ogunyemi ya sanar a ranar Litinin a Abuja, babban birnin kasar cewa, tuni kungiyar ASUUn ta kammala taron gaggawa na shugabanninta na kasar baki daya.

Biodun ya shedawa 'yan jaridu cewa, malaman ba za su shiga aji don koyar da dalibai ba, babu yin jarrabawa ko kuma wani taro da ya shafi ayyukan jami'o'in a dukkan rassan jami'o'in kasar, har sai gwamnatin kasar ta amince da biyan muradunsu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China