in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD yayi Allah wadai da harin ta'addanci a Najeriya
2017-08-16 16:28:29 cri
Sakatare jana na MDD Antonio Guterres yayi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kaddamar jiya Talata a Najeriya, wanda ya hallaka mutane 27.

A wata sanarwa da mai Magana da yawun sakatare janar din Stephane Dujarric ya fitar a daren Talata, yace mista Guterres ya bukaci a zakulo wadanda ke da hannu wajen aikata laifin a cikin Najeriyar da makwabtan kasashe, domin gurfanar dasu a gaban shari'a.

Hare haren biyu na ranar Talata a jahar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya yayi sanadiyyar hallaka mutane a kalla 27 da kuma raunatar wasu da dama.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China