A lokacin tattaunawar tasu, Xi ya nanata cewa, tattaunawar shugabannin biyu ta haifar da samun kyakkyawan sakamako wajen kara karfafa huldar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Amurka tun bayan ganawar da shugabannin biyu suka yi a Mar-a-Lago.
Haka zalika, an samu tsamin dangantaka tsakanin Sin da Amurka, kuma tuni kasar Sin ta riga ta bayyana matsayinta ga Amurkar, in ji shugaba Xi.
Shugaban kasar ta Sin ya nanata cewa kasarsa tana daukar batun kudurin Trump da muhimmanci musamman don tabbatar da cewa Amurkar za ta mutunta tsarin kasar Sin daya tak da ba shi muhimmanci.
Xi ya ce, kasar Sin tana fatan Amurka za ta kiyaye batun Taiwan bisa tsarin ka'idojin da suka dace da manufofin gwamnatin Sin daya taka da kuma mutunta yarjejeniyar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata. (Ahmad Fagam)