in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi da Putin sun amince da yin hadin gwiwa bisa manyan tsare tsare
2017-07-04 10:01:18 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ke ziyarar aiki kasar Rasha shi da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, sun gana a Moscow a ranar Litinin inda suka cimma matsaya guda domin karfafa hadin gwiwa don yin aiki tare game da batun zirin Koriya da kuma wasu manyan tsare tsare.

Kasashen Sin da Rasha sun kasance manyan aminai bisa yin hadin gwiwa kan muhimman batutuwa, kana abu ne mai matukar muhimmanci ga shugabannin biyu su kara musayar bayanai da kara hadin gwiwa game da tunkarar manyan tsare tsare, shugaba Xi ya bayyana hakan ne a yayin da suke musayar ra'ayoyi da mista Putin a Kremlin jim kadan bayan da ya sauka a birnin Moscow.

Bangarorin biyu za su karfafa hadin gwiwa, kana za su yi taimakekeniya a tsakaninsu domin kokarin samun ci gabansu tare, da kiyaye ikon kasashensu, da tabbatar da tsaron kasashensu, da burin ci gaban kasashensu, in ji shugaban na kasar Sin.

Ya kara da cewa, akwai bukatar su tsara wasu manufofi na tuntubar juna da yin aiki tare da juna game da muhimman batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da nufin warware manyan kalubalolin da suka shafi zaman lafiyar duniya, da kwanciyar hankali da samun ci gaban duniya baki daya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China