in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta kafa runduna ta musamman mai yaki da Boko Haram
2017-08-16 11:06:35 cri
A ranar Talata Najeriya ta kaddamar da wata rundunar tsaro ta musamman da nufin inganta al'amurran tsaro don yakar mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram, musamman a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Rundunar tsaron mai suna "special mobile strike force," wato rundunar tafi da gidanka ta musamman, an zabo dakarun ne daga rundunonin sojin kasar masu yawa, ana fata za su bullo da sabbin dabarun fatattakar mayakan na Boko Haram, kamar yadda Ibrahim Attahiru, kwamandan rundunar ya tabbatar da hakan a birnin Maiduguri dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar.

Attahiru, ya shedawa 'yan jaridu a Maiduguri, babban birnin jihar Borno cewa, kafa rundunar ta musamman ya zama tilas a matsayin sabon mataki da sojin kasar suka bullo da shi na kawo karshen ayyukan 'yan ta'adda na Boko Haram a kasar ta yammacin Afrika.

A cewarsa, dakarun da aka tura an ba su horo na musamman game da yadda za su yi amfani da sabbin dabarun yaki da ayyukan ta'addanci, wanda hakan zai ba su dama su murkushe mayakan Boko Haram, kuma su hana su duk wata damar samun 'yanci ko ta'ammali da kudade. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China