in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin saman Nijeriya ta kai hari maboyar Boko Haram a dajin Sambisa
2017-08-10 10:03:46 cri
Rundunar sojin saman Nijeriya, ta ce ta lalata wuraren ajiyar makaman da mayakan Boko Haram suke amfani da su a maboyarsu ta dajin Sambisa dake arewa maso gabashin kasar.

Cikin wata sanarwa da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Laraba, kakakin rundunar Olatokunbo Adesanya, ya ce rundunar 'Operation lafiya Dole' ta gudanar da binciken sirri da na sa ido a baki daya yankin Sambisa, al'amarin da ya kai ta ga gano wajen taruwar mayakan Boko Haram.

Olatokunbo Adesanya, ya ce aikin wani mataki ne na ci gaba da ayyukan fattatakar 'yan ta'addan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China