A yayin bikin maraba da zuwan tawagar, jagoran tawagar, Shen Hao ya bayyana cewa, ziyarar za ta taimaka wajen karfafa fahimtar juna tsakanin rundunonin sojojin ruwa na kasashen biyu da zurfafa hadin gwiwa da zamunci a tsakaninsu, ta yadda hakan zai habaka hadin gwiwar dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu.
A yayin ziyarar tawagar a kasar Tanzania, wakilan kasashen biyu za su yi shawarwari da mu'amala kan harkokin da abin ya shafa da gasa da atisayen hadin gwiwa da dai sauransu. (Maryam)