in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Kenyatta na Kenya da ya sake lashe zabe, ya yi alkawarin hada kan kasar
2017-08-12 12:41:59 cri
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da aka ayyana jiya da daddare a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, ya lashi takobin hada kan kasar, bayan babban abokin adawarsa, Raila Odinga ya yi fatali da sakamakon zaben ya na mai cewa an yi magudi.

Shugaban Hukumar zaben kasar Wafula Chebukati ya sanar da cewa, shugaba Kenyatta ya samu kuri'u miliyan 8.20 kwatankwacin kashi 54.27 na kuri'un da aka kada, yayin da Raila Odinga ya samu kuri'u miliyan 6.76 kwatankwacin kashi 44.74 na jimilar kuri'un da aka kada, al'amarin da ya kawo karshen zaman dakon sakamakon zaben da aka shafe kwanaki 4 ana yi.

Uhuru Kenyatta mai shekaru 55 zai sake mulkin ne a karo na biyu a kuma wa'adin shekaru 5 na karshe, kamar yadda kundin mulkin kasar ta tanada.

Da yake jawabin amincewa da sakamakon zaben, Shugaba Kenyatta ya lashi takobin hada kan kasar tare da aiwatar da ayyukan ci gaba da za su kyautata yanayin zaman al'umma.

Ya ce ya na son ya tuntubi babban abokin adawarsa wato Raila Odinga na Jam'iyyar National Super Alliance domin su gina Kenya a tare.

Gamayyar jam'iyyun adawa dai sun nuna kin amincewarsu da sakamakon zaben, suna masu cewa ba shi ne ainihin abun da al'ummar kasar ke muradi ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China