Babban sakataren kungiyar Mahboud Maalim, ya bukaci dukkannin bangarori masu ruwa da tsaki da su bi matakan da suka dace, da kuma yin amfani da hanyoyin da shari'a ta tanadar wanda ke kunshe cikin kundin tsarin mulkin kasar ta Kenya.
Sanarwar ta zo ne bayan barkewar tashin hankali a wasu sassan kasar ta Kenya, bayan da hukumar zaben kasar ta ayyana shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar a daren Juma'ar data gabata.
Jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben ne aka fara samun barkewar tashin hankali musamman a yankunan Kisumu da wasu sassan birnin Nairobi, inda 'yan adawa suka fi rinjaye.
A ranar Asabar, masu zanga zangar sun yi fito na fito da 'yan sanda a Kibera, inda aka dinga jin karar harbe harben bindigogi, kana an ga motocin daukar marasa lafiya na ta kai kawo a kan tituna.(Ahmad Fagam)