in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci a kauracewa sabbuban daka iya ruruta wutar rikicin bayan zaben Kenya
2017-08-14 09:36:51 cri
Kungiyar tarayyar Afrika AU, ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su kaucewa daukar matakai ko kuma yin wasu kalamai daka iya kara ruruta wutar rikicin bayan zabe a kasar Kenya.

Shugaban AU ya bukaci 'yan kasar da su mutunta tsarin doka da oda, bayan ayyana sakamakon karshe na zaben shugaban kasar a hukumance wanda aka gudanar da zaben a ranar 8 ga wannan wata na Augusta a kasar ta gabashin Afrika.

Shugaban kungiyar ta AU, Moussa Faki Mahamat, ya bayyana cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Kenya ta sanar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasar ne a ranar 11 ga watan Augusta, bayan kamala shi a ranar 8 ga watan nan, wanda tagawar masu sa ido a zaben suka bayyana shi da cewa yana da inganci kuma an gudanar da shi ba tare da yin magudi ba, daga cikin masu sanya ido a zaben har da kungiyar ta AU.

Faki, ya yi kira ga wadanda ba su gamsu da sakamakon zaben ba, da su kalubalance shi ta hanyar matakai na shari'a.

Shugaban na AU ya nuna damuwa game da barkewar tashin hankali a wasu yankunan kasar, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi masu yawa a kasar, sanarwar ta nanata cewa tashin hankali ba abu ne da za'a lamunce shi ba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China